ABNA24 : Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a yau din nan Alhamis inda ya ce: Alamu daga Amurka da Turai da ma sauran wajaje na daban suna nuni da cewa a halin yanzu dai duniya ta fahimci cewa kolin matsin lamba ba zai kai masu yinsa ga gaci ba, sannan kuma irin wannan matsin lambar zai zo karshe, alhali kuwa daga karshe dai al’ummomin da aka sanya su cikin wannan matsin lambar za su girbi abin da suka shuka na irin hakuri da juriyar tinkarar wannan matsin lambar.
Shugaban na Iran yana ishara da irin matsin lambar da Iran ta fuskanta ne cikin ‘yan shekarun nan daga wajen gwamnatin Amurka inda ya ce duk da irin wannan matsin lamba da takunkumi mai tsanani amma al’ummar Iran suna nan daram suna ci gaba da riko da tafarkinsu na ci gaba.
A jiya Laraba ma dai, a zaman majalisar ministocin na Iran, shugaba Rouhani ya bayyana cewar: Gwamnatin Amurka da take mafarkin ganin bayan Iran da kuma kawo karshen gwamnatin kasar sai ga shi ta fadi kasa warwas cikin wulakanci, wato shugaban yana ishara da kayen da shugaban Amurkan Trump ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin wulakanci da jin kunya.
342/